Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Zan Sauka Ba Har Sai Na Cika Wa’adin Shekara Hudu Kan Shugabancin PDP - Secundus


Uche Secondus, Shugaban Jam'iyyar PDP
Uche Secondus, Shugaban Jam'iyyar PDP

Gabanin babban taron jam’iyyar PDP, rikicin cikin gida na kara tsananta a cikin jam'iyyar a yayin da shugaban jam’iyyar Uche Secondus ya yi kememe cewa ba zai bar kujerarsa ba har sai ya kamalla wa’adinsa na shekara 4.

Majiyoyi daga cikin babbar jam’iyyar adawar sun alakanta yanayin rashin tabbas da ake fuskanta a cikin babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, da cewa ba ya rasa nasaba da furucin shugaban jam’iyyar Uche Secundus, da ya ce ba zai bar kujerarsa ba sai ya cika shekaru hudu cif-cif.

Haka kuma wasu majiyoyi daga cikin mambobin jam’iyyar da suka bukaci a sakaya sunansu, sun yi nuni da cewa Secondus ya yi biris da matsayar taron sulhu da jagororin jam'iyyar suka cimma makwanni 2 da suka gabata, inda ya ce muddin ba’a yi wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar garambawul ba, ba zai sauka daga kan kujerarsa ba.

Idan ana iya tunawa, a watan disambar shekarar 2017 ne aka zabi Uche Secondus a matsayin shugaban jam’iyyar ta PDP da sauran mabobin kwamitin gudanarwarta, a babban taron jam’iyyar da aka gudanar a dandalin Eagle Square a birnin tarayya Abuja.

A ka'ida kuma ya kamata wa’adin mulkinsa ya kare a watan Disambar shekarar nan ta 2021 da mu ke ciki.

Sai dai a cikin kasa da makwanni biyu da suka gabata ne wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ta PDP da aka fadada a Abuja, ya yanke shawarar katse wa’adin mulkin Secondus a watan Oktoba domin neman mafita ga rikicin cikin gida da ya ki ci ya ki cinyewa a jam’iyyar.

Taron ya sami halarcin gwamnonin jihohi, mambobin kwamitin amintattu wato BoT, tsoffin ministoci, tsoffin gwamnoni da wasu mambobin majalisar wakilai ta kasa inda suka umarci Secondus da ya kira taron kwamitin zartarwar jam’iyyar na kasa wato NEC, kwamitin da ya kasance na biyu mafi girma mai yanke shawara a PDP domin tabbatar da ayyukan da za su kai ga gudanar da babban taron jam'iyyar a watan Oktoba.

Gwamnonin PDP Sun Yi Taro A Makurdi
Gwamnonin PDP Sun Yi Taro A Makurdi

Sai dai makusantan Secondus sun shaida wa manema labarai cewa shugaban na PDP ya yi watsi da shawarar kawo karshen wa’adin mulkinsa a watan Oktoba.

Kazalika, wata majiya daga cikin jam'iyyar ta PDP ta bayyana cewa wani mamba daga arewa ya ce Secondus ya yi biris ne bayan tattaunawar da ya yi da wasu masu ruwa da tsaki a cikin jam’iyyar, inda ya ce dole ne ya kammala wa'adinsa na shekara hudu, daidai da tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar sashe na 47 sakin sashi na 1.

Sashe na 47 sakin sashi na 1 na kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP ya tanadar cewa duk shugabannin jam’iyyar daga matakin kasa, shiya-shiya, jihohi, kananan hukumomi zuwa ga gundumomi zasu rike mukaminsu na ofis na tsawon wa’adi daya na shekara hudu, kuma zasu iya neman wa’adi na biyu idan sun cancanta.

Sai kuma sashe na 47 sakin sashi na 2 da ya tanadi cewa a zaben shugabannin jam’iyyar na kasa zai kasance a babban taronta ne yayin da na wadanda ke matakin kasa kamar gundumomi zai kasance a sauran tarurruka jam’iyyar na kasa.

Mataimakin babban sakataren yada labaran Jam’iyyar PDP, Diran Odeyemi, dai ya shaida cewa akwai yiyuwar gudanar da taron kwamitin gudanarwar PDP a ranar talata don cimma matsaya kan lamarin da ya kunno kai.

XS
SM
MD
LG