Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Jam'iyyar PDP: Uche Secondus Ya Tsira


Gwamnonin PDP Sun Yi Taro A Makurdi.
Gwamnonin PDP Sun Yi Taro A Makurdi.

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Prince Uche Secondus ya tsira daga yunkurin kawarda shi daga kujerar shugabancin jam’iyyar da wasu ‘yan kwamitin zartarwa suka yi, a cikin wani rikicin cikin gida da ya barke a jam’iyyar.

A ranar Talata ne dai dukkan masu ruwa da tsaki a shugabancin jam’iyyar PDP a Najeriya suka tattaru, domin dakile wata takaddamar shugabanci da ta yi kokarin farraka babbar jam’iyyar adawar.

Lamarin ya kara kamari ne bayan da wasu ‘yan kwamitin zartarwa 6, sun kada kuri’ar kin amincewa da salon takun shugaban jam’iyyar na kasa a karkashin Uche Secondus, inda kuma suka yi kira gare shi da ya sauka daga mukaminsa nan take.

Shugabannin masu korafi na zargin Secondus da kasawa wajen tafiyar da lamurran ci gaba a jam’iyyar, da kuma haddasa baraka a dukkan matakai na jam’iyyar.

Uche Secondus, Shugaban Jam'iyyar PDP
Uche Secondus, Shugaban Jam'iyyar PDP

To sai dai a martanin da ya mayar, shugaban ya ce masu wannan da’awa, da ya kira “’yan tsiraru” ba su da wata hujja ta neman ya sauka daga mukaminsa, domin bai san ya aikata wani laifi da zai sa yayi hakan ba.

Duk wannan na zuwa ne kuma bayan da a makon jiya wasu shugabanni 7 suka gabatar da takardunsu na yin murabus daga mukamansu, bisa zargin shugaban da maida su saniyar ware a lamurran jam’iyyar.

To sai dai ganin lamarin na kokarin kasancewa, ya sa daukacin gwamnonin jam’iyyar na PDP, da kwamitin amintattu, da ‘yan majalisar tarayya da ma dukan tsofaffin gwamnoni da ministoci na jam’iyyar, suka hadu domin dakile wannan takaddama.

Gwamnonin PDP a wani taro da suka yi kwanan nan (Twitter/ PDP)
Gwamnonin PDP a wani taro da suka yi kwanan nan (Twitter/ PDP)

Shugaban gwamnonin PDP kuma gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, ya fadawa manema labarai cewa an sami cimma daidaito da bakin warware takaddamar, inda kuma aka bukaci dukkan bangarorin da ke takaddama, da su maida wukakensu kube domin ci gaban jam’iyyar.

Haka kuma an yi matsayar gudanar da babban taron zaben shugabannin jam’iyyar na kasa a cikin watan Oktoba, maimakon Disamba da aka tsara tun farko.

Taron ya kuma dorawa kwamitin zartarwa na jam’iyyar, da su kafa kafa kwamitoci 2, na shirya taron zaben shugabannin da kuma na tarin raba daidai na karba-karba.

Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal
Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal

To sai dai duk da yake an matso da babban taron zuwa watan Oktoba, da alama kuma za’a ba Secondus tare da sauran shugabannin jam’iyyar damar kammala wa’adin mulkinsu da zai kare a ranar 9 ga watan Disamban shekarar nan ta 2021.

To sai dai wasu majiyoyi sun bayyana cewa Secondus bai yi na’am da shawarar gudanar da taron ba a watan Oktoba, saboda yana ganin kamar ba zai yiwu a cikin lokacin ba.

Majiyar ta ce Secondus ya fada a wajen taron cewa ya shirya wasu tsare-tsare daga yanzu har zuwa watan Oktoba, domin daidaita al’amura a jam’iyyar, ciki har da tarukan zaben shugabannin jam’iyyar a duk fadin kasar.

XS
SM
MD
LG