A tattaunawa da manema labarai gabannin ziyarar da Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu zai kawo nan birnin Washington DC Laraban nan, jami'in yace "Amurka ba zata tilasta sharuddan da za'a bi a cimma zaman lafiyan ba."
A hukumance, matsayar Amurka kan wannan batu itace, Isra'ila da Falasdinu su raba yankin gida biyu, inda watakil- yankin Falasdinu zai mallaki zirin Gaza, da kuma illahiri- ko wani bangare na yammacin kogin Jordan, da kuma gabashin birnin kudus wanda Falasdinawan suke son ya zama helkwatar kasarsu idan har ta kafu. Haka nan ma MDD tana goyon bayan kafa kasaer Falasdinu a zaman hanyar warware rikicin na gabas ta tsakiya.