Shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum , ya ce ba haramun ba ne don ya nada dan tsohon shugaban kasar Mahamane Sani Issoufou a matsayin ministan mai.
Bazoum ya bayyana hakan ne yayin wata hira ta musamman da aka yi da shi a hedkwatar VOA da ke Washington D.C.
Shugaban na Nijar na halartar babban taron Amurka da shugabannin kasashen nahiyar Afirka, wanda shugaban Joe Biden ya shirya.
“Haramun ne, ba a iya nada shi? Na nada shi don ya kware, kuma don gwanintarsa kuma don yana dan Issoufou, duka wannan ba haramun ba ne, duka halal ne kuma ni nake da ‘yancin yin wannan. Kuma babu wanda zai hana ni na yi abin da nake ganin ya dace.” Bazoum ya fadawa Aliyu Mustapha Sokoto a hirar da suka yi.
“Ka san makiyanmu suna bakin ciki ba mu samu matsala ba tsakaninmu da Mahamadou Issoufou, ji suke yi wai idan suka yi irin wadannan maganganu za su bata tsakaninmu.”
Bazoum ya kuma kore ikirarin da wasu ke yi cewa jam’iyyar ta PNDS mai mulki ta rabu gida biyu kuma Issoufou ne yake jan ragamar gwamnatinsa ta bayan fage.
Da aka tambayi Bazoum ko zai sake tsayawa takara a zabe na gaba, sai ya ce, “tun yanzu? Ka san mai tsoron Allah ba ya yin irin wannan maganar.”
A bangaren yaki da cin hanci da rashawa, shugaban na Nijar ya kuma ce gwamnatinsa ta kama mutum akalla har 30 cikinsu har da minista.
A shekarar 2021 Bazoum ya lashe zabe a zagayen an biyu ya kuma kafa gwamnati karkashin jam’iyyar PDNS Tarayya inda ya gaji Issoufou wanda ya kammala wa’adin mulki biyu na shekara biyar-biyar.