Sai dai kuma Dirakta mai kula da kare shigowar cututtuka daga bakin iyakokin Najeriya Dakta Nasir Sani Gwarzo, ya zanta da Muryar Amurka inda yace, an samu sakamakon binciken mutuwar matashin wanda ya tabbatar da cewa ba cutar Ebola bace ta kashe shi.
Bayaninsa kan matakin da aka dauka na killace duk mutanen da sukayi mu’amula da matashin, matakine wanda yake anayinsa domin bada kariya ga al’umma da su kansu ma’aikatan kiwon lafiya, a duk lokacin da aka sami wata cuta da ake ganin tana da saurin yaduwa kamar su Ebola, ana dai ‘daukar ire-iren wannan matakan wani lokaci ba tare da mutane sun sani ba.
Kasancewar an sami matashin ne da zazzabi mai zafi hakan ne yasa aka ‘dauki matakin bincike don tabbatar da irin wutar da ta kashe shi , domin ana zargin cewa yana da cututtuka masu haddasa zazzabi da zubar jinni wadda ake kira Hemorrhagic Fever a turance. A safiyar yau Juma’a ne dai gwajin ya fito kuma an sami bayani cikakke cewa wannan cuta da ake zato ba cutar Ebola bace.
Yanzu haka dai an sassauta matakan da aka ‘dauka kan ma’aikatan lafiya, kuma ana fadakar da su kan dalilin da yasa akayi hakan sai a sallamesu.