Ana kallon wannan rana a matsayin wata gagarumar nasara ce wurin tabbatar duk al’ummar duniya suna samu ‘yancin su da Allah ya basu ba tare da la’akari da jinsi ko launi ko addini ko harshe ko siyasa ko zama namiji ko mace ko kuma yanayi da mutum ya tsinci kansa a ciki.
An yiwa bukin Ranar ‘yancin Dan Adam ta wannan shekara take “Matasa Su Tashi Tsaye A Kan ‘Yancin Dan Adam”.
Yunkurin da matasa zasu yi a wannan yaki da rashin mutunta ‘yancin dan adama a duk wani matsayi na rayuwa shine tubalin cimma hadin kai da zaman lafiyar al’umma. Lallai yakamata a yi amfani da basirar matasa kana a basu kwarin gwiwa su tashi haikan wurin ba wa kowa 'yancinsa daidai-wa-deda koda a ina suka kasance.
Batun ‘yancin dan adama ya hada da wasu abubuwa da dama, kama daga ‘yancin kasancewa ba tare da wani bambanci ba, da ‘yancin rayuwa da na tsaro da ‘yancin kasancewa cikin mutunci da sauransu kuma dukkanin su suna tattare a cikin kundin mulkin kasashe masu tasowa kamar kasar Najeriya da sauransu.
Al’ummar kasashe irin su Najeriya kan huskanci matsalolin tozartarwa daga hannun mahara ko kuma jami’an tsaro, musamman a shiyar arewa maso gabashin Najeriya inda ake fama da hare haren ‘yan ta’addan Boko Haram, lamarin da ya sabawa tanadin da dokokin kasar suka yiwa ‘yancin dan adam.
Ga dai Karin bayani a cikin rahoton da Haruna Dauda ya aiko mana a kan wannan rana:
Facebook Forum