Kamar yadda ba a rasa sani ba, kimanin makonni biyu da su ka gabata, Daraktan Hulda da Kafofin Yada Labarai na Kwamitin Yakin Nemar Zaben Jam’iyyar PDP na kasa Mr. Femi Fani Kayode ya yi zargin cewa Dantakarar Shugabancin Nijeriya karkashin Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari bai da takardar shaidar kammala makarantar Sakandare, al’amarin da ya haddasa takaddama tsakanin ‘yan jam’iyyun PDP da APC a gefe guda; da kuma tsakanin ‘yan Nijeriya wa daya gefen. Wannan ya sa Janar Buhari yin bayanin cewa ai kofin takardun ma na ofishin Sakataren kula da ayyukan sojoji na Sojin Nijeriya, kamar yadda tsarin aikin soja ya tanada. To amma jiya Talata sai kakakin Rundunar Sojojin Nijeriya Burgediya Janar Olajide Lalaye gaya ma wani taron manema labarai cewa rundunar ba ta da wani kofi na takardun shaidar kammala karatun Sakandari ta Janar Buharin.
Wakilinmu a Kano, Mahmud Ibrahim Kwari, wanda ya aiko wannan labarin, ya ce Dantakarar shugabancin najeriya a karkashin inuwar Jam’iyyar APC din, Janar Muhammadu Buhari ya Musanta zargin Jam’iyyar PDP din cewa, bashi da takardun shaidar kammala makarantar sakandare da kuma matsayin da rundunar sojojin najeriya ta dauka dangane da batun.
Wakilinmu Mahmud, ya ruwaito Buhari na shaida wa wani taron manema labarai cewa, “Na gaya masu cewa batun wannan makaranta ofishin Sakataren Soja, inda ni kaina na yi aiki a wurin, duk sojan da ya sami anini, wato ya zama ofisa na soja takardunsa su na nan daga lokacin da ya sami aninin har zuwa lokacin da ya fita; saboda haka na yi mamaki a yanzu ace wai wadannan takardun ba su wurinsu. To amma mun san abin da ya k e aukuwa a kasar nan. Wannan ya na nuna lalacewar aikin gwamnati.”
Da aka tambaye shi ko wadanne irin takardu ya yi amfani da su a zabukan baya da ya yi takarar Shugaban kasa sai ya ce a shekara ta 2003 da 2007 da kuma 2011, sai y ace to ai sai a je a tambayi INEC wannan tambayar. Sai y ace wai shin INEC sun bar shi ya yi takara a 2003 da 2007 da kuma 2011?. Buhari y ace wadanda su ka kammala karatun kwalejin Lardi ta Katsina tare a shekara ta 1961 sun hada da marigayi Janar Shehu Musa ‘Yar’aduwa da Mai Shari’a Umar Abdullahi, tsohon shugaban Kotun Daukaka Kara ta Nijeriya.