Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aung San Suu Kyi Ta Ce Kasarta Ba Ta Da Laifi


Suu Kyi Yyain Da Take Jawabi
Suu Kyi Yyain Da Take Jawabi

Shugabar Myanmar Aung San Suu Kyi ta kare kasarta kan sukar da ta biyo bayan zartas da hukuncin da kotun kasar ta yi ma wasu 'yan jarida biyu masu aiki ma kafar labaran Reuters makon jiya, wadanda aka tuhume su da laifin saba ma dokar kiyaye sirrin gwamnati, dokar da aka kafa tun a zamanin mulkin mallaka.

An kama Wa Lone da Kyaw Soe Oo tun a watan Disamban bara bayan ganawarsu da wasu jami'an 'yan sanda biyu a wani wurin cin abinci a Yangon inda aka ba su wasu kundin bayanai. Su na binciken kashe wasu Musulmin 'yan kabilar Rohingya su 10 da 'yan sanda da soja su ka yi a kauyen Inn Din bara. An yanke ma 'yan jaridan biyu hukuncin daurin shekaru 7.

Da ta ke magana a babban taron kasa da kasa kan tattalin arziki wanda ake yi a Hanoi, babban birnin kasar Vietnam, Aung San Suu Kyi ta yi kira ga duk wanda ya soki lamirin hukuncin tare da kiran a saki 'yan jaridar, ciki har da Mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence, da ya fito fili a bayyana inda aka yi rashin adalci a shari'ar.


Kungiyar kare hakkin Bil'Adama ta kasa da kasa Amnesty International, ta soki Aung San Suu Kyi saboda kare gwamnati kan hukuncin da aka yankewa 'yan Jaridar.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG