A look at the best news photos from around the world.
Duniyarmu A Yau

1
Yan matan Indiya sun yi kwalliyar awarwaro masu kala daban daban don kasancewa a cikin shagalin murnar zagayowar ranar 'yancin kasar a tagwayen biranen Secunderabad da ke Hyderabad

2
Sarki Akihito (Hannun Dama) da Sarauniya Michiko sun rusuna a dakin taro na Budokan dake birnin Tokyo ranar bikin cika shekaru 72 da mika wuyan Japanawa a lokacin yakin duniya na biyu don girmama mamatan da yakin ya lashe.

3
Nan wani Gleidson Hoffman ne dan asalin kasar Brazil ya kasa daurewa har ya fashe da kuka lokacin da ake bikin da aka yi a birnin New York na rantsar da baki 30 daga kasashen duniya 19 da suka zama Amurkawa.

4
Wani manomi a lokacin da yake ratsa wasu gonakin noman shinkafa a gundumar Sindhuli ta kasar Nepal.