Tun shekarar 2016 ya kamata a gudanar da zabe a Congo Kinsasha, amma sai hukumar zabe ta ce ba zai yiwu a gudanar da zaben ba, saboda tashin hankalin da ake fuskanta a yankin Kasar, kuma ana bukatar yiwa masu zabe rijista. Dadadden shugaban kasar Joseph Kabila, ya ki sauka daga kan mulki, duk da cewa wa’adin mulkin sa na biyu ya kare a watan Disamba.
Tunda farko hukumar zaben kasar sai watan Afrilun shekarar 2019 zata iya gudanar da zabe. ‘Yan adawa dai sun zargi shugaba Kabila da kokarin jan lokaci har sai yayiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, ya kawar da tsaida wa’adin shugabancin kasar.
A lokacin da ta kai ziyara Congo makon da ya gabata, jakadiyar Amruka a MDD Niki Haley, ta yi kira da a gudanar da sahihin zabe zuwa shekarar 2018, tana mai cewa Congo Kinshasa ba zata samu taimakon kasa da kasa ba, idan har ba a gudanar da zaben ba.
Mutane da yawa sun rasa rayukansu a zanga-zangar neman Kabila ya sauka daga kan mulki a karshen wa’adinsa kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
Facebook Forum