Harkoki sun ragu kwarai a kasuwannin saida hannayen jari a kasa da kasa a zaman maida martani ga matakin da kasuwar hada-hada da jeranta karfin hannayen jarin Amurka ta S&P ta bada sanarwar dauka wajen zaftare darajar karfin ruwan bashin da Amurka ke dashi.
Kididdigar da manyan kasuwannin hannayen jari a kasashen Asiya irin su Tokyo, da Hong Kong, da Seoul da kuma Sydney suka bayar, sunyi kasa da kusan kashi guda daga cikin dari zuwa kashi uku a budewar cinikayyar safiyar yau Litinin.
Kazalika,hannayen jarin masana’antu a birnin New York sun yi kasa tun ma kafin bude kasuwar shunkun “Wall Street”.
An kuma rufe kasuwannin hannayen jarin yankin gabas na tsakiya na karamin lokaci jiya lahadi, bayan da farashin hannayen jari suka fara yin kasa da kashi bakwai daga cikin dari a kasuwar shunkun birnin Tel Aviv.