ABUJA, NIGERIA - Shirin na wannan makon ya tattauna kan hanyoyin da za a dawo da zaman lafiya da hadin kai tsakanin al’ummar arewa da aka ci gajiyar hakan a zamanin da ya shude da ma gabanin zuwan turawan mulkin mallaka.
Shirin ya kuma tabo bangaren tarihi, tattalin arziki, da zaman tare da duk suka karfafa a zamanin baya ta hanyar jagororin gargajiya da suka dora yankin kan turbar da a ke tunawa da ita ta nasara.
Saurari cikakken shirin Nasiru Adamu Elhikaya: