Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AREWA A YAU: Ci Gaban Tattaunawa Kan Muhimmancin Hadin Kan ‘Yan Arewa Da Batun Yada Jita-Jita, Satumba 14, 2022


Nasiru Adamu El Hikaya
Nasiru Adamu El Hikaya

Shirin Arewa a yau na wannan makon ya ci gaba da tattanawa akan binciken ‘yan takara don ganin ayyukan da suka yi na taimaka wa al’umma.

ABUJA, NIGERIA - A ci gaban hirar da Nasiru Adamu El- Hikaya ya yi da Dr. Muhammad Bashir Sa’idu, mai sharhin ya ce ba shakka idan ‘yan arewa suka hada kansu to yankin zai samu ci gaba.

Ya kuma ce ya kamata ya yi ‘yan arewa zu fara maida hankali kan binciken abubuwan ciyar da al’umma gaba da masu neman takara suka yi kafin su zabe su, kama daga ayyukan jin-kai zuwa abubuwan da suka yi a lokacin da suke rike da wani mukami.

A gefe guda kuma, Abdullahi Manaja Bauchi, ya kara tofa albarkacin bakinsa kan batun yada jita jita ko farfagandar karya da wasu ke yi ta kafafen sada zumunta da nufin muzanta abokan hamayya.

Saurari cikakken shirin Arewa a Yau:

please wait

No media source currently available

0:00 0:09:52 0:00
XS
SM
MD
LG