Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Apple Zai Zuba Jarin Dala Biliyan 500 Tare Da Daukar Ma’aikata 20, 000 A Amurka


Hakan na zuwa ne bayan da Trump ya yi shelar aniyar Apple ta zuba jarin biliyoyin daloli a Amurka yayin da yake kwarzanta nasarar tsarin harajin da ya zo dashi wajen bunkasa tattalin arzikin Amurka.

A yau Litinin, kamfanin Apple ya sanarda cewar zai kashe fiye da dala bilyan 500 a Amurka a cikin shekaru 4 masu zuwa tare da daukar ma’aikata 20, 000, sanarwar da ake ganin zata yiwa Shugaba Donald Trump dadi wanda ke yiwa kamfanonin Amurka matsin lamba akan su dawowa da kere-kerensu gida.

“A yau Apple ya bayyana aniyarsa ta kashe kudade mafi girma, ta shirin kashewa da zuba jarin fiye da dala bilyan 500 a Amurka nan da shekaru 4 masu zuwa,” kamar yadda katafaren kamfanin fasahar sadarwar dake da mazauni a yankin “Silicon Valley” ya bayyana a cikin wata sanarwa.

A cewar shugaban kamfanin Apple Tim Cook: “muna da kwarin gwiwa game da makomar kere-keren Amurka, muna masu alfaharin dorawa akan jarin da muka jima muna juyawa a Amurka da wannan aniya ta zuba dala bilyan 500 domin dorewar makomar kasarmu.”

Haka kuma Apple yace zai dauke ma’aikata kimanin 20, 000, wadanda galibi zasu maida hankali akan fannonin bincike da cigaba da fasahar sadarwa da kirkirar sabbin manhajoji da kirkirarriyar basira da kuma koyarwa ta na’ura.

Sanarwar ta yau Litinin na zuwa ne bayan da Trump yayi shelar aniyar Apple ta zuba jarin bilyoyin daloli a Amurka yayin da yake kwarzanta nasarar tsarin harajin daya zo dashi wajen bunkasa tattalin arzikin Amurka.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG