Yayin da hukumar zaben jihar Taraba ke haramar gudanar da Zaben kananan hukukomi, a waje guda babbar jam’iyyar adawa ta APC, a jihar ne ke barazanar kauracewa zaben bisa zargin cewa da wata manufa aka saka zaben a wannan lokaci da ake fama da annobar cutar coronavirus.
APC, wacce a baya, ke sukar gwamnatin jihar game da rashin gudanar da zaben kananan hukumomin jihar , ta ce akwai abin dubawa game da zaben a yanzu.
Barr. Ibrahim El-Sudi tsohon dan majalisar wakilai kuma shugaban jam’iyar APC a jihar, a taron manema labarai da jam’iyar ta kira a jalingo fadar jihar, ya ce ba su amince da wannan lokaci da hukumar zaben ta saka ba.
Sai dai kuma a martaninta, hukumar zaben jihar Taraban, SIEC, ta ce tana nan daram game da ranar ta saka babu sauyi.
Dr Philip Wupe, Shugaban hukumar zaben ya musanta zarge-zargen da jam’iyyar APC a yanzu.
Shi ma dai gwamnan jihar Taraban, Darius Dickson Isiyaku ta bakin hadiminsa ta fuskaci harkokin siyasa Abubakar Bawa ya musanta zargin cewa gwamnatinsa ta shirya murda zaben.
Saurara karin bayani a sauti:
Facebook Forum