Jihar Wisconsin dake tsakiyar yammacin Amurka zata jira har zuwa akalla ranar Litinin don fitar da sakamakon zaben fidda gwani na shugaban kasa da aka yi a karkashin jam’iyyar Demokrat, wanda mutane suka fita kada kuri’a duk da barazanar yaduwar cutar coronavirus da ake fuskanta .
Jinkirin dai zai ba jami’an zaben isasshen lokacin tattara kuri’un wasu masu kada kuri'a da suka yi amfani da hanyar aika sakonnin wasika.
An rage adadin cibiyoyin zaben sosai a duk fadin jihar, daruruwan ma’aikatan zabe kuma sun ki su mutunta alkawarin da suka yi na yin aikin zaben, saboda tsoron kamuwa da cutar coronavirus a lokacin da suke duba sunayen masu kada kur’ia da basu yi rijista ba.
A Milwaukee, gari mafi girma a jihar, cibiyoyin zabe 5 a cikin 180 ne kadai aka bude. Amma an sami dogayen layuka da masu kada kuri’ar da suka rinka bada tazara a tsakaninsu a lokacin bude cibiyoyin zaben, a yayin da ma’aikatan lafiya suke ba jama’ar dake kan layukan takunkumin rufe hanci da baki.
Facebook Forum