Yanzu dai Majalisar Dattawa ta na zama kwanaki biyu ne a cikin mako daya, sannan Majalisar Wakilai kuma ta na zama rana daya ne tak a mako guda.
Wani babban hanzari da suka kawo wajen daukan wannan mataki ita ce barazanar da cutar coronavirus ke yi a kasar wanda yawan wadanda suka riga suka kamu suka kai 161,539 sannan adadin wadanda suka rasu sun kai 2,027.
An sallami kimanin mutane 147,581 daga Asibiti ya zuwa yanzu. Sanata Abdullahi Adamu ya ce wanan dalilin yana da karfin da zai sa a dauki wanan matakin domin akwai wadanda suka rasu, kuma an kaiyade yawan lokuta da mutane za su iya zama a wuri daya.
Saboda haka dole ne Majalisa ta bi umurni tare da bin dokoki da gwamnati ta gindaya domin kare lafiyar yan Majalisa saboda an samu yan majalisa da dama da suka rasu sakamakon cutar Covid-19.
A Majalisar Wakilai kuwa, mai magana da yawun Majalisar Benjaim Kalu, ya ce bullar annobar coronavirus ya sa dole Majalisar Wakilai daukan wannan mataki, duk da cewa an rarraba wuraren zama a zauren Majalisar Wakilan, amma yawansu da ya kai 360 shi ne ya sa aka ga cewa ba zai yiwu su zauna a wuri daya har na tsawon lokaci da kuma kwanaki ba.
Saidai kuma a dokance, wannan mataki tamkar tauye mudu ne ga 'yan Najeriya inji Kwararre a fanin kundin tsarin Mulkin Kasa Barista Mainasara Ibrahim Umar, wanda ya jaddada cewa kundin tsarin mulki ya tanadi cewa dukkan dan majalisa dole ne ya yi zama na kwanaki 2 bisa 3 na shekara daya, wanda shi ne ya kama kwanaki 180.
Barista Mainasara ya ce duk dan majalisar da bai kai yawan wadanan kwanaki ba, to kamata ya yi a tsige shi daga kujerar Majalisar, saboda haka yayi kira da su yi kokari su dauki matakan kare lafiya kamar yadda yakamata saboda su cika alkawalin da suka dauka tsakanin su da wadanda suke wakilta domin su yi dokoki da za su shawo kan rashin tsaro da kuma kare lafiyar yan kasa.
Babu shakka, cutar Covid-19 ta yi mummunan tasiri ga aiyukan Majlisar kasa idan za a yi la'akari da yawan kwanaki da za a rasa wajen zama da yan Majalisar ke yi a baya ga cewa kebabbun mutane ne ake basu izinin shiga harabar Majalisar, yayin da ake hana yan jarida da ma'aikata wadanda ba su sa takunkunmin baki ba daga shiga Majalisar.
Domin karin bayani saurari rahotan Medina Dauda.