Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce jami'anta a Nnewi, Jihar Anambra da ke kudu maso gabashin kasar, ta kama wasu mutane kimanin 34 'yan kungiyar tsagerun 'yan aware ta Biyafara wato (IPOB) ta 'yan kabilar Igbo zalla da ke kokarin ballewa daga Najeriya.
Rundunar ta ce jami'anta, tun da farko, sun sami bayanan sirri da ke nuna cewa tsagerun 'yan awaren da dama sun tattaru a wani yanki da ke cikin garin Nnewi inda su ke kokarin tayar da hankali, al'amarin da ya sa kwamandan 'yan sandan yankin ya jagoranci sauran jami'ansa don samar da tsaro.
Bayan jami'an 'yan sandan sun isa gurin ne kuma sai 'yan awaren su ka abka masu, inda su ka kashe sufeton dan sanda da ji wa wasu karin manyan jami'an 'yan sanda biyu rauni, ciki har da DPO, sannan kuma suka kone motar sintirin 'yan sanda yankin kurmus.
Ga Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton:
Facebook Forum