Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zargin Wani Dan Sanda Da Cin Amanar Abokan Aikinsa


Hukumomin 'yan sanda a Jihar Nassarawa su na binciken wasu 'yan sandan da aka ce sune suka tseguntawa 'yan kungiyar leken asirin Ombatse shirin kama madugunsu

Rundunar 'yan sanda a Jihar nassarawa ta soke shirin tattaunawa da 'yan jarida jumma'ar nan, bayan da rahotanni daga kafofi da dama suka kunno kai cewa an kama wani dan sanda dan kabilar Eggon dauke da bindigogi, kuma ana zarginsa, tare da wasu, da laifin tseguntawa 'yan kabilarsu ta Eggon shirin kamo madugun kungiyar asiri ta 'yan kabilar da aka yi niyya.

A yanzu hukumomin 'yan sandan sun ce sai asabar da rana, zasu tattauna da jarida domin ba su bayani kan inda aka kwana game da wannan binciken.

Kafofi da dama sun ce akwai alamun cewa wasu daga cikin 'yan sandan da aka tura domin kamo madugun kungiyar asisri ta Ombatse ta 'yan kabilar Eggon, sun tseguntawa mabiya wannan kungiyar abinda ake ciki, abinda ya ba su damar yin kwanton bauna tare da kashe 'yan sanda da dama.

Amma dai hukumomi sun ce wannan dan sanda dan kabilar Eggon da aka kama, an same shi da bindiga kwaya daya ce, amma ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano ko yana da hannu a wannan lamarin.

Halima Djimrao ta tattauna da wakilinmu a Jihar Nassarawa, Jibril Khalid, kan abubuwan da hukumomi suke fada musu.
Tattaunawa da Jibrin Khalid Kan Damke Dan Sanda Dan Kabilar Eggon - 2:35
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG