Rundunar 'yan sanda a jihar Bauchi tana tsare da wasu ma’aikatan gwamnatin jihar su biyar da ake zaginsu da karkata kudaden fensho na miliyoyin Naira, zuwa wasu asusun da suka kirkiro wanda bana hukuma ba ne kuma wanda su ke amfani dashi don amfanin kansu har na tsawon watanni masu yawa.
Kamar yadda bincike suka nuna, ma’aikatan suna aiki ne a hukumar fensho ta jihar da kuma kananan hukumomi, inda suke hadin baki ta hanyar cusa sunayen bogi a cikin jadawalin sunayen masu karbar kudaden fensho na wata-wata, wanda mai binciken kudade a hukumar fensho ke sanya wa a cikin jerin sunayen masu karbar kudaden fensho.
Kwamishinan ma’ikatar kudin jihar Bauchi, Alhaji Umar Adamu Sanda, ya shaida cewa wadannan ma’aikatan da ake zargi da karkata kudaden fensho da a ka yi, babban nasara ne ga gwamnati..
DSP Muhammed ya yi karin haske kan batun, da kuma bamu dama domin jin ta bakin mutanen da ake zargi da laifin karkata kudaden fensho zuwa wani asusu domin amfanin kansu.
Saurara cikakken rahoton Abdulwahab Muhammad:
Facebook Forum