A wata sanarwa da ya fitar a ranar litinin, ofishin babban mai gabatar da kara na Sudan yace an tuhumi Bashir da wasu mutane da laifin “ tunzura jama'a tare da kashe masu zanga-zanga.
A Ranar 11 ga watan Afrilu ne, Sojojin Kasar Sudan suka kawar da Al-bashir daga karagar mulki, bayan da aka shafe watanni hudu ana gudanar da gagarumar zanga-zangar adawa da shugaban da kuma yadda yake nuna bakin mulki a shugabancinsa.
Kungiyar kare hakkin bil'Adama sun ce, sojojin Sudan sun kashe masu zanga-zanga akallah sama da mutane 60.
An kulle Bashir a wani gidan kaso a birnin Khartoum mai cikakken tsaro, 'yan kwanaki bayan da aka hambare shi daga karagar mulki, bisa ga cewar danginsa, kuma ba a sake ganinshi a bainin jama’a ba tun lokacin.
Facebook Forum