Shugabar kasar Jamus Angela Merkel, ta shirya domin watakil jam'iiyyarta ta sha kaye, sakamkon manufofin gwamnatinta a kan bakin haure 'yan gudun hijira,a zaben da ake yi a wasu sassan kasar uku yau Lahadi.
Ana jin jam'iyyar da take adawa da karbar bakin haure, mai ra'ayin mazan jiya da ake kira AFD a takaice, zata taka rawar gani, a babban zaben da za'a yi a kasar tun bayanda hukumomi suka bude kan iyakokinta ga 'yan gudun hijira da bakin haure, su fiyeda milyan daya, a bara.
Fiyeda 'yan kasar milyan 12 ne zasu je rumfunan zabe domin kada kuri'unsu a zaben na yau.