Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Tuhumar Sojojin Najeriya 68 Kan Laifuka Daban-Daban


Ana Tuhumar Jami’an Rundunar Sojin Najeriya 68 Kan Laifuffuka Daban-Daban
Ana Tuhumar Jami’an Rundunar Sojin Najeriya 68 Kan Laifuffuka Daban-Daban

A Najeriya, yayin da wasu mayakan kasar ke fagen daga suna fafatawa da abokan gaba, wasu suna can hannu suna fuskantar shari'a akan wasu laifuka da ake tuhumar su akai.

ABUJA, NIGERIA - Wannan na zuwa ne lokacin da rundunar sojin ta kaddamar da kotun soji ta musamman domin hukunta jami'an ta 68 da ake tuhuma.

Matsalolin rashin tsaro da Najeriya ta samu kanta ciki tun daga matsalar Boko Haram a arewa maso gabas, na daga cikin abubuwan da suka kawo yawaitar jami'an soji yin cudanya da al'ummar kasa.

Duk da yake sojin suna da tsari da ka'idojin aiki, wasu lokuta ana samun korafe-korafe akan yadda suke gudanar da ayukan nasu, yayin da rundunar ke kafa kotu ta musamman don kulawa da laifuka da ake tuhumar jami'an da aikatawa.

Wannan karo rundunar sojin Najeriya ce ta kaddamar da kotun da za ta yi shara'a ga jami'an ta 68 a Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya, akan laifuka daban daban.

Kwamandan yanki na takwas na sojin Najeriya da ke da hedkwata a Sokoto, Manjo Janar U. U. Bassey, ya ce an kafa kotun ne don gaskiya ta yi aikinta akan laifukan da ake tuhumar jami'an.

Ana Tuhumar Jami’an Rundunar Sojin Najeriya 68 Kan Laifuffuka Daban-Daban
Ana Tuhumar Jami’an Rundunar Sojin Najeriya 68 Kan Laifuffuka Daban-Daban

Akan haka ya yi kira ga kotun da ta yi bincike tare da auna karfin hujjojin da za'a gabatar kuma ta yi aiki bisa ga tsarin baiwa kowa dama a lokacin binciken kararrakin.

Ya kara da cewa, wannan kotun ba za ta fuskanci katsalandan ba daga ko'ina ba, don haka wadanda ake tuhuma da laifuka suna da cikakken lokaci na kare kansu ko su kira wadanda za su taimaka musu.

Honourable Godwin Uwadiye lauya ne ga jami'an sojin, ya kuma ce laifukan da ake tuhumar su duk da yake yanzu suna zaman maras laifi, sun hada da nuna tsoro, duk da yake ya ce ba ya son zurfafa magana akan sojin da aka yi wa kwanton bauna kuma ake tuhumarsa da tsoro, kasancewa batun na gaban kotu.

Sauran laifuka sun hada da bacewar wasu kaya sanadiyyar harin da aka kai wuraren zamansu'

"Amma dai mun zura ido mu ga yadda za ta kaya, muna kuma fatar ganin an hanzarta shara'ar wasu daga cikin sojojin sun kasance tsare fiye da wata 7 wasu wata 22 wasu 18 wasu ma shekara 2."

Sai dai abin jin dadin shi ne, lauyiyin da ke tsayawa sojojin da yawansu ‘yan rajin kare hakkin bil'adama ne, za su yi iya kokarinsu ganin kotun ta yi adalci.

To ko yaya masharhanta ke kallon wannan zaman da kotun soji ke yi son yin shara'a ga jami'an ta? Detective Auwal Bala Dorumin Iya shugaban sashen nazarin aikata laifuka da tsaro a jami'ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano ya ce akwai abin dubawa.

A cewarsa, hakan zai taimaka mutanen gari su kara yadda da hukumomin soja kuma za su samu ilimin kai kara idan soja ya aikata ba daidai ba, su ma sojojin za su shiga taitayinsu ganin cewa yanzu jama'a sun san ana iya hukumta su kuma zai taimaka ga samun kyakkyawar mu'amala.

Kaddamar da wannan kotun dai shi ne irin sa na uku a Sokoto, an yi wasu biyu a watan Satumbar bara da Afrilun wannan shekara.

Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:

Ana Tuhumar Sojojin Najeriya 68 Kan Laifuka Daban-Daban
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

XS
SM
MD
LG