Kudurin dokar da za ta haramta binciken shugabanin Majalisar Dokokin Kasa ta raba kawunan yan majalisar tun kafin a kai ga mika ta ga Kwamitin da zai bude mata fagen saurare a Majalisar Wakilan Najeriya, kamar yadda wakiliyar Sashin Hausa Medina Dauda ta aiko a wannan rahoton.
Wannan kudurin doka da Onorabil Odebunmi Olusegun ya gabatar a zauren Majalisar Wakilai yana neman a yi wa sashe na 308 na kundin tsarin mulkin kasa garambawul domin a ba shugabanin majalisar dokokin kasa kariya har tsawon zamansu a Majalisar, wai domin su samu damar yin ayyukansu cikin natsuwa. Amma daga dukan alamu kawunansu sun rarrabu, saboda su na bayyana ra'ayoyi mabanbanta akan kudirin.
Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya ce yana goyon bayan dokar idan har an samu kafa ta domin yana ganin dokar ba kawai ta kakakin Majalisa ba ce ba ta Shugaban Majalisar Dattawa ba ce, amma don a tsare Majalisar ne gaba daya tunda ita ce kashin bayan demokradiyya , don haka idan doka za ta kare Shugaban kasa da Gwamnoni ina ga Shugabanin Majalisa domin su yi aikinsu?
Amma shi kuwa Tajuddeen Abbas ya ce bai ga amfanin kariya ga ‘yan majalisa ba, domin ai su, sun zo yi wa alumma aiki ne, ba sa bukatar wata kariya, su ne ya kamata su yi dokokin da za su kare ‘yan kasa, kuma wanan shi ne aikin da aka za6e su akai.
Manazarci kuma kwararre a kimiyyar siyasa ta kasa da kasa Farfesa Usman Mohammed na Jami'ar Baze da ke Abuja, ya kula cewa kariya tana sa shugabani kaucewa, domin Gwamnoni da suka more kariya sun yi amfani da kariyar ne suka dare kujerun Majalisa domin su cigaba da mulkan mutane, amma demokradiya ta bada dama na hana a ci mutuncin mutum,sanan ta bada dama a hukunta wanda duk aka kama da laifi.
Wannan ra'ayi shi ne daya daga cikin Shugabanin Gamaiyar Kungiyoyin Matasa na Arewa Sheriff Nastura Ashir ya amince da shi, inda ya ce kamata ya yi Majalisa ta yi dokar da za ta kwaye rigar kariyar ne tun daga sama har kasa domin yana sa shugabani suna wuce gona da iri.
Shi ma Malami a Kwalejin ilimi da ke Azare, Mohammed Bello Nawaila, ya ce kuskure ne a ce ba za a binciki shugaba ba sai ya gama mulki; yin haka ba daidai ba ne domin wannan irin yunkuri shi ne ya hana a samu cin nasarar yaki da cin hanci da rashawa a kasar.
Ga Madina Dauda da cikakken rahoton:
Facebook Forum