Shugaban Majalisar Wakilai a Najeriya, Femi Gbajabiamila yayi wanan furucin ne a daidai lokacin da Majalisar ke fara aiki akan kasafin kudin shekara 2021 da Shugaba Mohammadu Buhari ya mika wa Majalisar.
Kakakin ya ce, lallai sai an biya diyar wadanda aka yi zargin ‘yan sanda sun kashe a kasar tun shekaru 10 da suka wuce kuma har ila yau sai an biya Kungiyar malaman jami'o'i da a halin yanzu suke yajin aiki dukannin kudaden da aka yi masu alkawalin za a biya tun a zamanin gwamnatin da ta shude.
Wani abu da Shugaban Jamiyar Accord, Mohammadu Lawal Nalado yace akwai abin dubawa a wannan furuci na Kakakin Majalisar domin idan ba a sa hannu a kasafin kudi ba, yana nufin ba za a yi wa 'yan kasa aiki ba ke nan, kuma yana kira ga gwamnati da ta dauki matakin tabbatar da amincewa da wanan kasafin kudi saboda a tsira daga matsalolin da akasin hakan ka iya jawowa.
A nashi nazarin, tsohon ma'akacin gidan rediyon BBC kuma a yanzu mai nazari akan al'amuran yau da kullum Bala Ibrahim, ya ce irin wanan furuci da ya fito daga bakin kakakin majalisar wakilai kuma daya daga cikin jigajigan Jamiyar APC mai mulki abin takaici ne.
A ganinsa idan har an biya masa bukata a ta hanyar biyan diyar da ya fada, to Bala ya ce yana da jadawalin mutanen sama da dubu daya na shiyar Arewa da tashin hankali ya same su kuma yake ganin su ma sai an biya masu diya.
Abin jira a gani shi ne yadda za ta kaya a zauren Majalisar bayan an kamala aiki akan kasafin kudin na shekara 2021.
Saurari Cikakken Rahoton Medina Dauda cikin sauti:
Facebook Forum