Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Shirin Rantsar Da Alkalan Da Za Su Saurari Shari’ar Yunkurin Tsige Trump


'Yan majalisar wakilai da ke jagorantar shirin tsige Trump a lokacin da za su gabatar da kudurinsu a majalisar dattawa a ranar Litinin
'Yan majalisar wakilai da ke jagorantar shirin tsige Trump a lokacin da za su gabatar da kudurinsu a majalisar dattawa a ranar Litinin

Ana shirin rantsar da ‘yan Majalisar Dattawan Amurka a matsayin alkalai da kuma masu taimaka musu a shari’ar tsige tsohon shugaban kasa Donald Trump. 

A yau Talata ake shirin rantsar da su a wani mataki na ci gaba da tuhumar tsohon shugaban saboda Mamane majalisar dokoki da magoya bayansa suka yi.

Sai dai ba za’a fara yin shari’ar ba har sai ranar 8 ga watan Fabrairu, bayan da shugabannin ‘yan Democrat da na ‘yan Republican a Majalisar Dattawan suka amince da a jinkirta.

Matakin yin hakan shi ne, don ba da isasshen lokaci ga dukkan bangarorin biyu na ‘yan Majalaisar Wakilai wanda za su zama a matsayin masu gabatar da kara da kuma tawagar lauyoyin Trump don su shirya kare shi.

Karin lokacin zai bawa Majalisar Dattawan damar tabbatar da karin wadanda shuguba Joe Biden ya nada a matsayin ‘yan Majalisar zartarwarsa.

A dai yammacin jiya Litinin, ‘yan Majalisar Wakilai wadanda za su kasance masu gabatar da kara a shari’ar suka yi tattaki zuwa zauran Majalisar Dattawa don kai kudurin da ya ke tuhumar Trump da tunzura magoya bayansa su mamaye ginin Majalisar Dokokin Amurka a farkon wannan watan na Janairu.

Wannan hatsaniya ta sa ‘yan Majalisar sun yi ta neman mafaka don tsira da ransu, lamarin da har ila yau ya yi sanadin mutuwar mutum biyar.

XS
SM
MD
LG