Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bada umurnin aiwatar da shawarwarin da tsohon Shugaban Ma'aikata a zamanin mulkin Goodluck Jonathan Stephen Orosanye ya bayar ta yi wa ma'aikatu da hukumomin Gwamnati garambawul.
Kwamitin, wanda aka kaddamar a shekara 2011, ya mika rahotonsa a shekara 2012 inda ya bada shawarar a hada ko kuma a sauya ko a hade wasu ma'aikatun wuri guda a yayinda ya bayyana hanyoyin tafiyar da ayyukan Gwamnati a Najeriya a matsayin daya daga cikin mafi tsada. Kwamitin ya bada shawarar rage hukumomi da doka ta kafa a Najeriya daga 263 zuwa 161.
Babban mai ba Ministan Kudi shawara a harkar hulda da manema labarai Yunusa Tanko Abdullahi ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta dauki wannan mataki domin kudaden shigowa na gwamnati sun yi karanci, kuma ma'aikatun gwamnatin suna da yawa sannan yawancinsu ayyukansu kusan iri daya ne, shi ya sa gwamnati ta yi wannan hobbasa, kuma an rataya aikin a wuyan Sakataren Gwamnatin Tarrayya ne.
Ana yi wa rahoton lakabi da rahoton Orosanye kuma yana dauke ne da shafuka 800 kuma ya bada shawarar soke wasu hukumomi ko gwamutsa su wuri daya, wani abu da Barista Maimuna Yaya Abubakar ta ce yunkuri ne mai kyau domin zai rage yawan kudin da ake kashewa akan ma'aikatun sannan wadanda aka gwamutsa kuma ana iya dauke su zuwa wasu jihohi domin a rage yawan masu shigowa cikin Birnin Tarayya domin yin hulda da su.
Kwamitin ya jadadda cewa Ma'aikatun suna bukatar dinbin kudade wajen gudanarwa, to ko idan an rage su kwaliya za ta biya kudin sabulu? Tambayar kenan da na yi wa kwararre a fanin tattalin arziki Shuaibu Idris Mikati, sai ya ce idan aka dauki mutum miliyan 200 ko fiye da haka, za a ga cewa ma'aikatan ba su wuce miliyan biyar ba, amma in aka duba kudin da ake kashewa wurin gudanar da su sai a ga cewa suna kashe kusan kashi 60 cikin 100 na kasafin kudin kasar na shekara, kuma yanzu tattalin arzikin kasar ya ragu sosai.
Tun da dadewa ne kwararru suke ta shela tare da ba gwamnati shawarar ta dauki irin wanan matakin, gashi yanzu dole ya sa ta duba. Tsohon Shugaban Ma'aikata a zamanin Goodluck Jonathan Stephen Orosanye shi ne ya shugabanci kwamiti din tare da wasu mutane guda 7 wadanda Goodluck Jonathan ne ya kafa su. Rahoton ya dade a ajiye ba a yi komi dashi ba sai yanzu.
Ga Madina Dauda da cikakken rahoton:
Facebook Forum