Dan kasar Najeriyar nan da ake zargi da yunkurin neman tarwatsa wani jirgin saman Amurka na jigilar fasinjoji da boma-boman da ya boye a cikin kamfan shi, ya bayyana a gaban wata babbar kotu a jiya talata, inda cikin kangara ya kara jadadda biyayya ga al-Qaida a daidai lokacin da ake shirin fara shari’ar ta shi a birnin Detroit.
A cikin wasu kalaman da ya furta a gabannin shigowar alkali cikin kotun, Umar Farouk Abdulmutallab ya lashi takobin cewa ‘yan gwagwarmayar Islama za su ga bayan Amurka, sannan kuma ya fada da kuwa cewa “Anwar ya na nan da rai”, a nan ya na magana ne game da Anwar al-Awlaki Ba’amurken nan Musulmi mai tsattsauran ra’ayi, wanda aka kashe makon jiya a kasar Yeman cikin wani harin jiragen saman da aka kai.
Ranar Kirsimetin shekarar 2009 aka kama Umar farouk Abdulmutallab, bayan da fasinjoji su ka fi karfin shi su ka danne shi lokacin da boma-boman da ya boye a cikin kamfan shi su ka ki tashi a cikin jirgin saman kamfanin Northwest wanda ya taso daga Amsterdam zuwa Detroit.
Abdulmutallab na fuskantar tuhumar aikata manyan laifuffuka takwas da su ka hada da gama bakin aaikata ta’addanci. Jami’an Amurka masu gudanar da bincike sun yi amanna cewa a kasar Yemen Abdulmutallab ya samu horo da shawarwari daga wurin ‘yan al-Qaida, a cikin su har da Anwar Awlaki.
Umar Farouk Abdulmutallab ya ki amsa laifin da ake tuhumar shi da aikatawa sannan kuma ya yanke shawarar kare kan shi da kan shi a matsayin lauya, tun a watan satumba ya kori lauyoyin shi da kotu ta ba shi.