Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Samun Karin Yawan Yara a Makarantun Jihar Borno


'yan makaranta
'yan makaranta

Tabarbarewar tsaro da rashin kula da makarantu ya sa wasu iyaye suka janye 'ya'yansu daga makarantu a jihohin dake karkashin dokar ta baci musamman jihar Borno

Gwamnatin jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya kuma daya daga cikin jihohi uku dake cikin dokar ta baci ta ce cikin shekaru biyun da ta kama mulki ana samun karin yawan yaran makaranta a jihar sabanin shekarun baya.

Kwamishanan ilimi na jihar Alhaji Musa Inuwa Kubiyo ne ya bayyana hakan a wata firar da ya yi da wakiliyar Muryar Amurka Sa'adatu Fawu. Ya ce sun yi wasu abubuwa a makarantu da suka jawo hankalin iyaye lamarin da ya sa suka soma dawo da 'ya'yansu makaranta. Da sai iyaye sun tallafawa 'ya'yansu amma yanzu gwamnati ta dauki nauyinsu dari bisa dari. Gwamnati ta gyara gidajen kwana da na daukan darusa da na malamai. Kusan kashi saba'in da biyar bisa dari na tsofofin makarantu aka sabunta. Ban da haka an kuma gina wasu sabbi.

Dangane da ilimin mata kwamishanan ya ce gwamnati ta mayarda hankali kan iliminsu. A wasu makarantun ma mata sun fi yawa. Amma akwai wasu sassa na jihar inda har yanzu ilimin boko nada koma baya domin gurguwar fahimta da aka yi ma ilimin. Bugu da kari wadanda suka anfana da ilimin boko daga wadannan sassan basu koma wuraren nasu ba yadda mutanensu zasu yadda da su su faminci alfanun ilimin. Sabo da haka gwamnan jihar zai kafa wani kwamiti na musamman ya zagaya wadannan sassan ya wayar wa mutanen wurin kawunansu a kuma dubi matslarsu. Ya ce a zahiri gaskiya akwai rashi wanda damuwa ne domin suna anfani da 'ya'yansu wurin biyan bukatunsu na yau da kullun. Yanzu gwamnati zata biya ma iyayen bukatunsu domin su bar yara su je makaranta. Misali kowane uba ya kai dansa makaranta za'a bashi tallafi domin ya bar dansa ya cigaba da makaranta. Su kuma yaran za'a ciyar dasu a makarantu a yi masu sutura a kuma kula da lafiyarsu. Idan kuma zasu cigaba da karatunsu gwamnati zata dauki nauyinsu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Shiga Kai Tsaye
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG