WASHINGTON, D. .C - Sassan Kenya sun shiga wani muhimmin mataki na samar da rigakafin cutar zazzabin cizon sauro na farko a duniya, da kuma samun raguwar mace-mace ga yara ‘yan kasa da shekaru 5.
Ma'aikatar lafiya ta Kenya dai ba ta bayyana lokacin da za a samar da rigakafin a fadin kasar ba.
Ana samun babban tasiri cutar a yankuna masu tsananin zafi kamar gabar tekun Indiya a Kenya, da wuraren da ake samun yawan ruwan sama kamar yankin yamma da ke kusa da Lake Victoria.
Kasar Kenya na da kimanin mutum miliyan 5 da suka kamu da zazzabin cizon sauro sannan sama da 12,000 suka mutu a shekarar 2022, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya.
Yawancin wadanda abin ya shafa dai yara ne ‘yan kasa da shekara 5 da kuma mata masu juna biyu.
Kasar Kenya na ci gaba da yaki da cutar zazzabin cizon sauro ta hanyoyin gargajiya kamar rarraba gidajen sauron masu dauke da maganin kwari a jikinsu, da fesa wuraren kiwo, da inganta saurin gano cutar da bada magani, amma kwararru sun ce wadannan hanyoyin da ake ci gaba da yaki da cutar sun kai iyaka.
Masanin kula da lafiyar jama'a Dr. Willis Akhwale, mai ba da shawara na musamman ga Majalisar kawo karshen zazzabin cizon sauro ta Kenya, ya ce annobar cutar COVID-19 da ta hana rarraba magunguna da bada kulawa.
Ya ce ana bukatar sabbin hanyoyin magance cutar saboda wasu ‘nau’in cutar da ba a samun sauki da ake samu a sassan Afirka.
“Muna bukatar mu fara duba saka hannun jari a sabbin magunguna. Hakan ya kamata ya iya hana duk wata juriya a nan gaba mai zuwa,” inji shi.
Akhwale ya ce sauran bukatu sun hada da karin kudade da tallafin kayan aiki.
-AP
Dandalin Mu Tattauna