Yau Lahadi ake yin zabe jin ra'ayi mai sarkakiya a kasar Girka. Ba'a dai tantance ba dada ko 'yan Girka zasu jefa kuri'a yin na'am ga kara tsuke bakin aljihun gwamnati domin samun ranche daga turai na ceton tattalin arzikin kasar, ko kuma su yi watsi da bukatan kungiyar kasashen turai, su fuskanci kasadar a fitar dasu daga cikin kasashen dake amfani da takardun kudin Euro.
Prime Ministan kasar ya bukaci 'yan kasar da suyi watsi da ka'idodin da aka gitta musu da suka hada har da kara haraji da kuma rage kudin da gwamnati ke kashewa. Yace yin watsi da bukatun ya baiwa yan kasar matsayi mafi ingancin yin shawarwari da Ministocin kudin kungiyar kasashen turai.
Prime Ministan yace, shi da yan kasar da dama su dandana daga bukatun kungiyar kasashen turai, na hasarar aiyukan yi da sauran matsaloli.
Shi kuma Ministan kudi na kasar ya zargi kungiyar EU da laifin ta'adanci ta hanyar tsoratar da yan kasar Girka domin su jefa kuri'ar yin na'am da sharuddan data gitta.
Su kuma masu goyon bayan kungiyar EU, sunce kasar Girka bata zabi, fayace kasancewa cikin kungiyar EU. Suka ce idan aka tilasta Girka fita daga cikin ayarin kasashen da suke amfani da takardan kudin Euro, hakan na nufin kasar Girka ta koma ga amfani da takadan kudin drachma, da wasu kasashen kila su ki yarda ai amfani da takardan kudin a cikin kasar su.
Yau Lahadi ake yin zabe jin ra'ayi mai sarkakiya a kasar Girka. Ba'a dai tantance ba dada ko 'yan Girka zasu jefa kuri'a yin na'am ga kara tsuke bakin aljihun gwamnati, ko kuma su yi watsi da bukatan kungiyar kasashen turai,.