Jiya Laraba a jamhuriyar Afirka ta tsakiya, 'yan kasar suka je rumfunan zabe, domin kada kuri'a a zaben kasar da aka sha jinkirtawa, wanda mutane da dama suke fatar zai kawo karshen tarzomar da ake yi shekaru uku ana fama da ita a kasar.
Anga dogayen layuka a Bangui babban birnin kasar, kodashike akwai rahotanni ba'a bude wasu rumfunan zabe akan lokaci ba, duk da haka babu rahotannin anyi arangama ko magudi ba.
An tsananta matakan tsaro a zaben shugaban kasa da 'yan majalisar, da aka shiry za'a yi tun farko ranar Lahadi, amma aka dage da kwanaki uku saboda matsaloli jigilar kayan aiki da kuma kimtsawa.