Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Cigaba da Samun Tashe tashen Hankula a Iraqi

Daya daga cikin motocin da aka yi kunar bakin wake da ita a Iraqi

Jiya Lahadi an kai akalla hare haren kunar bakin wake uku a Iraqi inda kurdawa hamsin suka rasa rayukansu.

An cigaba da samun tashe-tashen hankula a Iraqi Jiya Lahadi, inda a kalla jami’an tsaron Kurdawa 50 ne aka kashe a hare-haren kunar bakin wake guda 3, da kuma wannan hafsin ‘yan sanda da nakiyar gefen titi ta kashe a lardin Anbar mai zaman lafiya.

Boma-boman da aka saka a cikin motoci sun fashe ne a harabar ofishin gwamnatin Iraqi dake arewa da garin Baquba kusa da Qara Tappah, yayin da tsofaffin sojojin Kurdawa suke gabatar da kawunansu domin komawa aikin soji. Jami’ai sunce daya daga cikin ‘yan harin kunar bakin wake ya tayar da bom dinsa ne a bakin kofar harabar ofishin gwamnatin, inda motoci biyu shake da boma-bomai suka biyo baya mintuna kadan. A kalla mutane 60 ne suka ji raunuka a wadannan hare-hare.

Wani jami’i a majalisar garin Qara Tappah mai suna Salahddin Baban ya gayawa sashen Kurdanci na Muryar Amurka cewa fashe-fashen suna da girma matuka, kuma sun kashe mutane dake mitoci 100 daga inda suka tashi. Ya kara da cewa wadannan fashe-fashe sun lalata ma’aikatu uku sannan sun kashe mutane a cikin wadannan ma’aikatu.

Sa’o’i kadan bayan hare-haren ne kungiyar mayakan ISIL ta dauki alhaki, inda ma ta kara da cewa ‘yan harin kunar bakin waken wasu mutane uku ne wadanda ba ‘yan asalin Iraqi bane suka kaisu.

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG