Kakakin rundunar sojojin Najeriya Kanal Sagir Musa, ya shaida wa manema labarai cewa babu wasu sojojin kasar Chadi ko na wata kasa dake bangaren Najeriya ta zirin yankin tafkin Chadi ko ma wani bangaren Najeriya.
Kanal Sagir ya kuma ce da sanin Najeriya dakarun Chadi suka fafata da 'yan Boko Haram a ta bangaren tafkin Chadi, a wani mataki na girmama ci gaban hadin kan kasashen yankin tafkin Chadi a karkashin inuwar rundunar dakarun kawancen yankin, wato MNJTF.
Wannan na zuwa ne biyo bayan ikirarin da rundunar sojojin Chadi ta yi, inda kakakinta Kanal Azem Banadoua Agouna ke cewa dakarun Chadi sun kora ‘yan Boko Haram har tsibiran dake yankunan Najeriya da Nijer.
Kanar Sagir Musa ya tabbatar da cewa duk yake-yaken da dakarun Chadi suka yi da 'yan Boko Haram a cikin Najeriya da goyon bayan kasar aka yi, bisa fatan hakan zai hana 'yan Boko Haram samun maboya a yankin Chadi inda suke kaddamar da hare-hare akan Najeriya.
Saurari Karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum