Sojojin da suke goyon bayan shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara suna can suna neman mayakan da suka goyi bayan tsohon shugaba Gbagbo a birnin Abidjan. Talata nan sojoji suka kai wadanda ake zargi otel din Golf inda ake tsare da Mr Gbagbo da matarsa da kuma sauran mukarrabansa. A wani wuri dabam kuma, a birnin Abidjan anyi harbe harbe jefi jefi da manyan bindigogi da kuma sace sace. Sojojin da suke goyon bayan Ouattara suna okarin kama yan yakin sa kan Gbagbo matasa, musamma ma shugabansu Charles Ble Goude wanda da shine Ministan harkokin matasa a zamanin mulkin Gbagbo. Mr Ouattara yayi kira ga dukkan mayakan kasar da su sajiye makamansu tunda an riga an kama Mr Gbagbo. Litinin din nan aka kama Mr Gbagbo bayan da ya shafe fiye da watani hudu yana una taurin kai yaki ya yarda cewa ya sha kaye a zaben shugaban kasar da aka yi. A wani jawabi daya gabatar ta gidan talibijin a daren litinin, sabon shugaban na Ivory Coast yayi kiran a samu zaman lafiya a kasar ta Ivory Coast wadda tayi watani tana fama da tarzomar bayan zabe data zama sanadin mutuwar daruruwan mutane kuma dubbai suka arce daga gidajensu. Mr Ouattara wanda shekarunsa sittin da tara ya kuma lashi takobin kafa wani kwamitin gano gaskiya da sasantawa domin hukunta wadanda aka samu da laifin keta hakokin jama'a da wasu laifuffukan. Ofishin kula da kare hakkin jama'a na Majalisar Dinkin Duniya ya fada cewa an kashe akalla mutane dari biyar da talatin da shidda a fafatwar da aka yi kwanan nan a yammacin Ivory Coast
Sojojin dake goyon bayan shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara suna neman mayakan da suka goyi bayan tsohon shugaba Gbagbo a birnin Abidjan. A yau talata sojoji suka kai wadanda ake zargi otel din Golf inda ake tsare da Mr Gbagbo da matarsa da kuma sauran mukarrabansa.