Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Barazanar Azawa Iran Sabbin Takunkumi


Wani kwararre yake aiki a wata masana'anatar tace Uranium na Iran.
Wani kwararre yake aiki a wata masana'anatar tace Uranium na Iran.

Ingila da Faransa da Jamus sun fada laraban nan cewa za a kakabawa Iran karin takunkumi idan taki ta bada hadin kai da hukumar hana yaduwar makaman kare dangi.

Ingila da Faransa da Jamus sun fada laraban nan cewa, za a kakabawa Iran karin takunkumi idan taki ta bada hadin kai da hukumar hana yaduwar makaman kare dangi, domin hukumar ta bada sahihan bayanai cewa Farisa tana kokarin kera makamin Nukiliya.

A cikin rahoto da hukumar ta sake jiya talata, ta bayyana matukar damuwa kan bayanai da suka nuna cewa Iran tayi aiki kan kera makaman Nukiliya, har da gwaji kan sassan makamin.

A wani gangami da aka nuna ta talabijin laraba, shugaban Iran Mahmoud Ahmadinejad, ya fada cewa “Iran fa ba gudu ba jadabaya, kan shirin Nukiliyar kasar”.

Rahoton ya kunshi zargi mafi tsanani kuma dalla dalla cewa shirin Nukiliyar Iran na soja ne. A kalaman da yayi yau laraba shugaba Ahamdimejad yayi watsi da rahoton cewa ya kunshi “ikirarin Amurka da bashi da tushe”.

Har sau hudu Majalisar Dinkin Duniya take kakabawa Iran takunkumi, sabo da taki ta tsaida shirin Nukiliyar kasar da za a iya amfani dashi na farin hula da kuma soja.

Manyan kasashe dake yammacin Duniya sun ce suna kokarin hana Iran mallakar makaman Nukiliya, Farisa kuma ta dage cewa shirinta na farar hula ne.

Duk da haka Rasha ta fada cewa ba zata goyi bayan a kakabawa Iran wani sabon takunkumi ba.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG