Sakataren gwamnatin jamhuriyar Nijar Dakta Gandu Zakara, shine ya gabatar da sunayen mambobin sabuwar gwamnatin shugaban kasar ya nada, watanni biyu da rabi kenan bayan da ya sanar da shirin kafa gwamnatin hadin kai a wani matakin hada kan ‘yan kasar Nijar, domin tabbatar da tsaro da barazanar ‘yan ta’adda.
Gwamnatin mai mambobi 43 ta kunshi take galibi da ministocin gwamnatin da ta gabata. Kamar yadda dayawa daga cikin ke ci gaba da rike mukamansu a gwamnatin da shugaba Isufu ya kafa a farkon wa’adin mulkinsa na biyu, missali kamar ministan cikin gida Bazu Mohammed ko ministan bunkasa ayyukan Noma Albadé Abouba ko Ibrahim Yakuba na harkokin kasashen waje da dai sauransu.
Wani abin lura a wannan karon shine an canzawa ministan tsaro Hassoumi Massaoudou matsayi zuwa ma’aikatar kudi ta kasar, yayin da ministan kiwon lafiya Kalla Muntari ke maye gurbinsa a ma’aikatar tsaro.
Haka kuma an samu shigowar wasu kusoshin jam’iyyar MNSD Nasara a sabuwar gwamnatin. Daga cikin ministocin 43 da sabuwar gwamnatin ta kunsa za a iya ganin mata 8 wanda hakan ke nufin an mutunta tsarin dokar da ta kebe kashi 20 cikin 100 na duk wani mukamin shugabanci ga matan jamhuriyar Nijar. Sabanin yadda abin ya kasance a ranakun farkon gwamnatin da ta gabata, lamarin da wancan lokaci ya haifar da tayar da jijiyar wuya daga kungiyoyin kare hakkin mata. Sai dai an wannan karon akwai karancin matasa a sabuwar gwamnatin da shugaba Issoufou Mahamadou yayi wa suna gwamnatin hadin kai.
Domin karin bayani ga rahotan Sule Mumuni Barma daga Nijar.