Hotuna da wasu sakonnin bidiyo da dai sauransu sun nuna yadda 'yan Najeriya da wasu ma daga kasashen Afirkan kan tsinci kansu cikin takaici a Saudiya.
Hakan ko na faruwa ne sakamakon shiga kasar ta Larabawa domin neman aikin yi.
Zargin azaftar da matan Afirka a Saudiya na kara ta'azzara saboda hatta kungiyar hadin kan Afirka, wato AU, a zamanta na baya bayan nan ta tabo batun inda ta nemi kawo karshen bautar da 'yan Afirka ke shiga a Saudiya.
Amina Umar Al-Hammadi wata 'yar jihar Borno dake zaune a Saudiya ta tabbatar da fadawar mata cikin garalin. Ta ce masu kawo matan kan fada masu cewa indan sun je Saudiya ga kudaden da za'a basu alhali kuwa ana bautar dasu ne. Ta kara da cewa wulakancin da suke fuskanta ya wuce iyaka. Babu abinci, kana ga duka da zagi. An mayar dasu tamkar awaki.
Amina ta gargadi hukumar Najeriya ta toshe hanyar kawo 'yan kasar a wulakance. Injita, su da suke kasar zasu taimaka amma gwamnatin Najeriya ma ta tashi ta taimaka. Ta hana masu safarar mutane da suke kawosu.
Muhammad Sani Inusa karamin jakadan Najeriya a Saudiya ya ce suna da labarin ana bautar da 'yan Najeriya a Saudiya. Suna bincike. Kawo yanzu sun gano kamfuna biyu dake kawo mutane. Daya shi ne Said Kamfani kuma a wurinsa sun samu sunayen mutane 450 da suka kawo. Yanzu suna bin mutanen daya bayan daya suna tattara baya nai. Inji Inusa da zara sun gama zasu mikawa ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta san matakan da zata dauka.
Ga rahoton Nasiru Adamu El Hikaya da karin bayani.
Facebook Forum