Jami’ai a Ethiopia, sun ce mai tsaron lafiyar Babban Hafasan sojin kasar ta Habasha ya harbe shi har lahira, sa’o’i bayan da jami’ai suka ce an yi yunkurin juyin mulki a jihar Amhara.
Mai magana da yawaun Firai Ministan Habasha, Abiy Ahmed, ta ce an kashe shugaban dakarun Chief Sear Mekonnen da wani janar mai ritaya a wasu hare-hare da aka kai a gidan Sear.
“Al’umar kasar nan, ba ta bukatar gwamnatin da ke danne hakkokin mutane, da yin kisa, cikin shekarun da suka gabata, mutanen Ethiopia sun nuna cewa, ba sa son gwamnati mai mulkin kama karya.” Inji Firai ministan Ahmed.
Mai magana da yawun firai ministar a jiya Asabar ta ce “wani gungun masu kisa” ya kutsa kai cikin wani taro da ake yi a babban birnin Amhara, inda ya kashe shugaban yankin Ambachew Mekonnen da wani mai ba shi shawara.
Kafafen yada labaran kasar sun ruwaito cewa, shugaban jami'an tsaron jihar ta Amhara, Janar Asamnew Tsige ne ya jagoranci yunkurin na juyin mulki.
Bayanai sun yi nuni da cewa, tuni an kama mai tsaron lafiyar da ya kashe shugaban dakarun kasar, amma har yanzu ba a ga Janar Asamnew ba.