An yi wa manhajar sada zumunta ta WhatsApp mallakar kamfanin Facebook kutse, a cewar shugabannin kamfanin.
WhatsApp ya yi kira ga daukacin masu amfani da manhajar wacce akalla mutum biliyan 1.5 ke amfani da ita, da su sabunta manhajarsu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
Kamfanin bai bayyana adadin mutanen da kutsen ya shafa ba, amma ya ce ya shawo kan lamarin, inda ya bukaci mutane da su sabunta manhajar ta WhatsApp a wayoyinsu.
Manhajar ta WhatsApp, kan yi tunkaho da irin kwararan matakan da ta dauka wajen sirranta duk wani bayani da ke cikinta.
Yadda Kutsen Ya Faru
Masu kutsen sun kirkiri wata manhaja ce da suke dasawa a wayoyin masu amfani da manhajar ta WhatsApp domin kwasar bayanai.
Hakan ya kan ba su damar yin kutse, inda sukan iya leken asirin wayoyin masu amfani da manhajar ta WhatsApp.
Masu kutsen sukan kira lambar wanda suke so su tatsi bayanansa, sai su kwashi bayanan da suke bukata, ko da mutum bai amsa wayar ba.
Su kan kira mutane ne ta manhajar ta WhatsApp, a cewar jaridar Financial Times, wacce ta ce ita ta fara gano matsalar.