Gwamnonin da suka halarcin zaman sun hada da na jihohin Neja, Kaduna, Taraba, Nasarawa, Binwai, da kuma Adamawa. Ko bayansu akwai Sufeto Janar na 'Yansanda, da shugaban Ma'aikatar Tsaro na farin Kaya, da Shugaban Hukumar Leken asirin kasa. Kusoshin tsaron sun kwashe sa'o'i kimanin bakwai suna nazarin hanyoyin magance matsalolin tsaro dake damuwar kasar.
Mahalarta taron sun amince cewa za horar da jami’an tsaro na musamman wanda za a kirasu “Agro Rangers” da yawansu zai kai dubu biyar da nufin sa ido a duk rikicin da ake yi a dazuzzukan kasar. Ministan Harkokin Cikin Gida Dambazau ya yiwa wakiliyarmu Madina Dauda karin haske inda ya tabbatar mata da cewa, tuni aka zabo wadannan jami’an tsaro dubu biyar ana jiran kudi ne kawai aje a horar da su a kan aikin da za su yi.
Shima gwamnan jihar Taraba Darius Dickson Ishaku yace jihar na kokarin hana kiwo kuma ya kare dokar da ya kafa dangane da kiyo a jihar, inda yace dokar ba zata cutar da kowa ba kuma hukuma zata samarwa makiyaya ciyawa da ruwa da zasu yi anfani da su wajen kula da dabbobinsu.
Facebook Forum