Dayake Kirista a fadin duniya na cigaba da shagulgulan Ista (Easter), abokin aikinmu Mahmud Lalo ya tuntubi Rabaran Yawa Aho Tsiga na Majami’ar ECWA da ke garin Tsiga na Karamar Hukumar Dutsin –Ma ta jihar Katsina, wanda ya ce ranakun sun bi juna kusa da kusa, kuma kowanne da muhimmancisa. Ya ce ranar Jumma’a ce aka gicciya Annabi Isa; ranar Lahadi kuma aka tabbatar da ya tashi daga matattu; sannan yau kuma Litini, ita ce kuma ranar da ake murnar tashin Yesu Almasihu daga matattu da kuma bayyanarsa a wurare da dama, wanda hakan ya dada tabbatar da tashin nasa.
Rabaran Tsiga ya ce dalilin tashin Yesu Almasihu daga matattu shi ne ya kawo nasara ga rayuwar Kirista ta bangaskiya. Ya ce wannan tashi na Yesu na tabbatar ma Kirista cewa wata rana shi ma zai tashi daga matattu kamar yadda Annabi Isa ya tashi. Da abokin aikinmu Mahmud Lalo ya tambaye shi ko wadanne irin ayyukan ibada akan so mutum ya yi a rana ta yau, sai Rabaran Tsiga ya ce da farko dai ya kamata Kowane Kirista ya je masujjada ya yi sujjada ga Ubangiji ya gode wa Allah saboda fansarsa da Allah ya yi. Wato saboda Allah ya aiko Annabi Isa ya fanshi dan adam, kowane Mai-bi zai je Ikiliziyarsa ya yi wa Allah godiya; za a kuma ziyarci ‘yan’uwa, kuma da kyau idan an dafa abinci don wannan murnar a bai wa makwabta da kuma mabukata cikin kauna da farin ciki.
Rabaran Tsiga ya ce ana kuma iya ziyartar ‘yan fursuna a karfafa su, a ba su abinci a kuma karanta masu maganar Allah; ko kuma a je asibiti a gaida marasa lafiya a gaishesu a ba su gudunmowa a kuma yi masu addu’a. Wadannan ne ire-iren abubuwan da ya kamata ace Mai-bi ya yi a lokaci irin wannan.
Da Mahmud ya tambaye shi ko wace shawara ya ke da ita ga wadanda kan mai da rana iran wannan ta bushasha, sai Rabaran Tsiga ya ce duk wanda ya yi amfani da wannan lokaci wurin yin bidi’a, ko wani jin dadi na sabon Allah kamar shaye-shaye da dai sauransu, to bai yi wa Allah godiya ba, ya zama butuli; kuma ya yi haka ne domin radin kansa amma ba don abinda Allah ya masa ba. Rabaran Tsiga y ace duk wanda ya yi amfani da wannan lokacin wurin aikata masha’a to zai gamu da fushin Allah.