Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jana'izar Tandja Mamadou a Nijar


Tandja Mamadou
Tandja Mamadou

A Jamhuriyar Nijar an yi jana’izar tsohon shugaban kasa Tandja Mamadou a fadar shugaban kasa inda daruruwan mutane suka hallara.

Jama'a da dama sun hallara ne domin yin ban-kwan karshe kafin a isa da gawarsa a garinsu na haihuwa wato Maine Soroa da ke jihar Diffa inda za a yi masa sutura.

Dazu da hantsi a farfajiyar fadar shugaban kasar Nijer aka ajiye gawar tsohon shugaban kasa Tandja Mamadou .hukumomin koli da iyalai da dangi da aminan mamacin sun hallara domin yi masa bankwanan karshe..

Bayan jawabin ban girman da tsohon fra minista Maman Oumarou ya gabatar shugaba Issouhou Mahamadou ya rusuna a gaban gawar Tandja Mamadou da nufin girmamawa kafin daga bisani ya isar da gaisuwar ta’aziya ga iyalan mamacin.

Manyan jami’an kolin kasar Nijer na jiya da na yau sun halarci wannan taro da ya hada jana’iza da bukin karramawa. Tsohon shugaban kasa Mahaman Ousman wanda ya shugabancin majlisar dokokin kasa a tsawon shekaru 10 na mulkin Tandja ya bayyana juyayi akan wannan rashi.

Shi ma shugaban jam’iyar PNDS Tarayya Bazoum Mohamed dake sahun ‘yan siyasar da suka je yiwa marigayi Tandja Mamadou bankwana ya jinjinawa kamun ludayinsa.

Kulawar da tsohon shugaban kasar ta Nijer ya baiwa jama’ar karkara tun yana soja har I zuwa lokacin da ya ajiye kakinsa domin shiga harakokin siyasa sun kara masa kima da farin jini a idon ‘yan kasa inji wani dadaden abokin tafiyarsa Ali Sabo kusa a jam’iyar MNSD NASARA wace ta dora Tandja akan karagar mulki.

tsohon fra minista Maman Oumarou da ke magana cikin hawaye saboda yadda wannan mutuwa ta girgiza shi yace rasuwar Baba Tandja ba wai iyalensa kawai ta mayar marayu ba ‘yan kasa baki daya ne suka fada cikin halin maraici saboda yadda ya sadaukar da rayuwarsa wajen ganin kasa ta ci gaba.

Daga bisani an nufi garin Maine Soroa dake jihar Diffa da gawar marigayi Tandja Mamadou inda za a yi masa sutura kamar yadda ya bada umurni a lokacin da yake raye.

Kaunar da jama’ar Nijar ke yiwa wannan bawan Allah ya sa wasu mazaunan birnin Yamai jerawa bakin hanyar da ke zuwa filin jirgin sama domin yi masa bankwanan karshe.

Shugaba Tanja Mamadou mai shekaru 82 a duniya ya rasu ne a ranar talatar 24 ga watan November a babbar asibitin yamai ya bar mata 2 da ‘yaya 10.

XS
SM
MD
LG