Shugaban Jamhuriyar Nijar, Shugaba Issouhou Mahamadou ya jagoranci jana’izar sojoji 71 da suka rasu a sakamakon harin ta’addancin da ya rutsa da su a ranar Talatar da ta gabata a barikin sojan Inates daura da kan iyakar kasar Mali.
A farfajiyar barikin sojan sama na Escadrille da ke birnin Yamai ne aka yi jana’izar wadannan sojoji kimanin 71 da su ka rasu a barikin sojan Inates.
An shafe sa'o'i ana ana gwabza fada da wasu maharan da aka kiyasta cewa sun kai daruruwa.
Shugaban kasar Nijar ya russuna a gaban mamatan ya yi masu jinjinar ban girma da bankwana.
"Laftana Kanar Hassan Anoutab kai da askarawanka 70 kun nuna jarumtaka saboda haka mutuwarku sadaka ce". inji shugaban.
Ya kara da cewa mutum ya rasa ransa saboda kare martabar kasa dauke da makami a hannu, wani abu ne da za a dauka a matsayin kyakkyawan karshe.
Ya ce koda yake iyalanku suna cikin jimamin rashi amma kuma ‘ya'yanku za su yi alfahari da kasancewar iyayensu jarumai ne.
Domin karawa jami’an tsaro azamar aiki a wannan lokaci na yawaitar hare haren ta’addanci, shugaban na kasar Nijar ya yi karin girma ga dukkan sojojin da suka rasu sanadiyyar wannan hari na barikin Inate.
Kuma a cewar Ministan tsaro, Farfesa Issouhou Katambe, "yaki, ba gudu, ba ja da baya".
A karshe an nufi makabartar Yantala ta birnin Yamai inda aka bizne gawarwakin wadannan sojoji.
Reshen kungiyar IS a Sahara, a karkashin shugabancin Adnane Abu Whalid Al Saharaui, ya dauki alhakin kai harin na barikin Inates, wanda karo na biyu kenan a shekarar nan ta 2019.
Rasuwar wadannan dakaru na ci gaba da girgiza jama’a.
Saurari cikakken rahoto cikin sauti.
Facebook Forum