Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci jami’an tsaron kasar da jami’an tsaro na leken asiri da su kara kaimi wajen dakile ayyukan matatun mai biyo bayan mutuwar gomman mutane da daren Juma’a bayan fashewar wata haramtacciyar matatar mai a dajin Abaezi da ke karamar hukumar Ohaji-Egbema a jihar Imo.
Da yake mayar da martani ga abin da ya bayyana a matsayin “musiba da bala’i ga kasa baki daya,” Shugaba Buhari ya ce alhakin asarar rayuka da dukiyoyi dole ya hau kan masu daukar matatar man ta haramtacciyar hanya, “kuma dole ne a kama su a kuma a hukunta su.
Buhari ya mai da martanin ne a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu ya fitar wacce Muryar Amurka ta sami kwafinta.
Da yake mika sakon ta'aziyya game da lamarin ga iyalan wadanda lamarin ya shafa, al'ummar Ohaji Egbema da ma gwamnati da jama'ar jihar Imo, shugaban ya bukaci shugabannin al'umma, 'yan sanda, da jami’an lekan asiri da kada su sake barin faruwar irin wannan lamarin mai ratsa zuciya a duk fadin kasar.