Wasu ‘yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne domin neman kudin fansa, sun yi awon gaba da kimanin mutum 40, ciki har da wani basaraken gargajiya a jihar Niger.
Maharan sun yi garkuwa da mutanen ne a yakuna daban-daban da ke jihar, inda wannan al’amari ya faru daga ranar Asabar din da ta gabata zuwa jiya Litinin.
Daga cikin wadanda aka yi garkuwan da su, har da wani basarake.
Satar mutanen ta shafi garuruwan Bandogari, Kokoki da Kokawo, da ke kanana hukumomin Rafi da Sarkin Fawa.
Dukkanin kananan hukumomin, sun hada iyaka da jihar Kaduna, wacce ke fama da matsalar satar mutane.
“Tsakani da Allah yara da mata yanzu muna kwana a cikin jeji ne, saboda zaman dadar da ake yi.” Inji wani mazaunin daya daga cikin garuruwan, wanda ya nemi a sakaya sunansa.
Wani mazaunin garin bandogari ya shaidwa Muryar Amurka cewa “abin da ya faru a Bandogari shi ne, masu garkuwa da mutane sun sace mutane akalla 13.”
Sai dai da aka tuntubi Kakakin ‘yan sandan jihar ta Niger, DSP Abubakar Dan Inna, sai ya ce a ba shi lokaci zai kira, amma har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto bai kira ba.
Saurari cikakke rahoton Mustapha Nasiru Batsari daga Minna: