Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yankewa Tsohon Shugaban Afirka Ta Kudu Zuma Hukuncin Wata 15 a Kurkuku


Tsohon Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma, zaune a Babbar Kotun Afirka ta Kudu
Tsohon Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma, zaune a Babbar Kotun Afirka ta Kudu

An umarci tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya shafe watanni goma sha biyar a gidan yari bayan kin bayyana gaban kwamitin dake gudanar da bincike kan jerin zargin cin hanci da rashawa da aka tafka lokacin da ya ke shugaban kasa.

Kotun kundin tsarin mulkin kasar ce ta yanke hukumcin yau Talata bayan ta same shi da laifin yi wa kotu karan tsaye. Babbar kotun ta umarci Zuma ya kai kanshi ga ‘yan sanda cikin kwanaki biyar.

Kotun ta umarci Zuma dan shekaru 79 ya bayyana gaban wani kwamitin bincike na musamman farkon wannan shekarar, da ke bincike zarge zarge da dama da ake yi wa tsohon shugaban kasar da suka shafi wawashe kaddarorin gwamnati a tsawon wa’adin mulkinsa tsakanin shekara ta 2009 zuwa 2018.

Zuma ya musanta zarge zargen ya kuma ki ba kwamitin hadin kai. Yana zargin mukadashin babban alkalin kasar Raymond Zondo shugaban kwamitin binciken da yi mashi bita da kulli.

Binciken da ake yi wa Zuma na daga cikin matakan da shugaban kasa mai ci yanzu Cyril Ramaphosa ya dauka na yaki da cin hanci da rashawa a gwamnatin kasar da kuma jam’iyar ANC mai mulki.

XS
SM
MD
LG