Makon da ya gabata ne gwamnatin hadakar Sudan, ta tabbatar da dokar nan da ta samu goyon bayan Firai Minista Abdalla Hamdok, dake cewa duk wanda ya aikata kaciyar mata zai fuskanci daurin shekaru uku a gidan yari, sannan a ci shi tara.
Kungiyoyin kare hakkokin mata sun yi marhabi da sabuwar dokar, amma kuma sun nuna damuwa cewa mawuyacin lamari ne a sake tunanin ‘yan Sudan su daina kaciyar mata, saboda al’ada ce da suka yi imani da ita cewa kafin su aurar da ‘ya’yan su mata.
Daraktan kungiyar Equality Now, Faiza Mohamed ta ce dokar haramta kaciyar mata tana da muhimmanci wurin tsawatawa. Sai dai ta kuma ta ce wadanda suka yi imani da ala’adar ba zasu kai karan masu yi, ko kuma su yi yunkurin hanawa koda kuwa sun san ana yi.
Facebook Forum