Sabon fadan da ya barke a Jihar Central Equatoria dake Sudan ta Kudu a wannan satin, na gurgunta yarjejeniyar zaman lafiya mai cike da sarkakiya da kasar ta cimma.
Wani mai magana da yawun kungiyar ‘yan tawaye ta NAS ya ce wata hadakar dakarun soji da ta hada da sojojin gwamnati da tsofaffin mayakan kungiyar SPLM-IO, ta kai hari kan wasu wuraren kungiyar NAS a Jihar ta Central Equatoria tun daga ranar Lahadi.
“Sun je sun kai hari kan sansanoninmu a Senema, da ke yankin unguwar Ombaci, da kuma Mediba a yankin garin Morobo, sannan sai Kajo-Keji Kala. Hakazalika sun kai hari kan dakarunmu kuma mun maida martani,” abin da mai magana da yawun kungiyar mayakan ta NAS, Samuel Suba, ya fada kenan a wani shirin Muryar Amurka game da Sudan Ta Kudu mai suna South Sudan in Focus.
Facebook Forum