A cewar wasu mutane biyu dake da masaniya kan shirye-shiryen amma wadanda basa son a ambaci sunayen su.
Ana sa ran wannan taron zai faru ne a a lokacin ziyarar da shugaba Trump zai kai kasashen Turai a cikin Wata mai fita, har ma ana nunin cewa mai yiyuwa ne su hadu kafin babban taron kungiyar tsaron Turai ta NATO da za’ayi ran 11 ga watan Yulin ko kuma bayan ziyarar da shugaba Trump zai kai Biritaniya kwannaki biyu bayan an kamala taron na NATO.
Sai dai fadar White House ta shugaban na Amurka taki cewa uffan kan wannan batu, kamar yadda ita ma Hukumar Tsaron Amurka taki tace komai kan maganar a lokacinda gidan rediyon VOA ya tuntube ta.
Facebook Forum